16 Oktoba 2024 - 17:50
Adadin Shahidai A Gazza Ya Kai Mutane Dubu 42 Da 409

A cikin sa'o'i 24 da suka gabata gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hari sau 6 a zirin Gaza, wanda a sakamakon haka mutane 65 ne suka yi shahada sannan wasu 140 suka jikkata.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa: Tare da samun wadannan shahidai, adadin shahidai a Gazza tun bayan fara aikin guguwar Aqsa ya kai mutane dubu 42 da 409 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai dubu 99 da 153".